Shirin samar da abinci a Indiya

Abinci
Image caption Ana kokarin samar da abinci mai rahusa a Indiya

Wani shirin samar da abinci a farashi mai sauki na fiye da dala biliyan goma sha takwas ga talakawan Kasar Indiya ya sami hayewa a majalisar wakilan Kasar.

Ana dai yaba Wannan shirin samar da abincin a matsayin wani mahimmin mataki na kawadda yunwa da kuma rashin abinci mai gina jiki da suka addabi 'yan Kasar.

Sai dai dole ne sai kudurin dokar ya samu hayewa a majalisar dokokin Kasar kafin ya zama doka.

Idan hakan ta faru, shirin zai samar da tallafi a shinkafar da ake ci da kuma alkama, ga kusan kashi saba'in cikin dari na al'ummar Kasar sama da mutum biliyan daya

Karin bayani