Farashin mai ya yi tashin gwauron zabo

Mai
Image caption Rikicin Syrian ya kuma shafi Kasuwannin hannayen jari.

Farashin mai ya yi tashin gwauron zabo a duniya cikin watanni shida sakamakon damuwa game da halinda Syria ke ciki.

Damuwar ita ce tashin hankalin dake bazuwa zuwa wasu bangarori na yankin gabas ta tsakiya zai kawo cikas ga samar da man yankin, ko kuma ya yi illa ga jigilar man daga yankin kogin Fasha.

Yankin gabas ta tsakiya ne ke samar da kashi daya bisa ukun na man da ake samarwa a duniya.

Rikicin na Syrian harwa yau ya shafi Kasuwannin jari.

Karin bayani