Dakaru na jiran umurnin Obama a kan Syria

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama

Sakataren tsaron Amurka, Chuck Hagel ya shaidawa BBC cewar dakarun kasar a shirye suke idan har Shugaba Obama ya basu umurnin kaddamar da matakin soji a kan Syria.

Mista Hagel ya ce an kai wasu kayayyakin soji zuwa wani waje don jiran ko wacce shawara shugaban zai yanke.

A cewarsa, ta bayyana karara gwamnatin Syria ce ke da alhakin kai hari da makamai masu guba a makon daya gabata, amma ya ce Amurka za ta jira ta kuma tattance bayanan sirri don nuna gaskiyar lamarin.

Pirayi Ministan Birtaniya, David Cameron ya kira Majalisar dokoki daga hutunta don gudanar da mahawara a kan matakin da Birtaniya za ta dauka game da tashin hankalin.

Mai magana da yawun Pirayi Ministan ya ce Birtaniya na cikin shirin ko-ta kwana a kan irin matakin sojin da za ta dauka.

Manyan kawayen Syria, wato Rasha da Iran da China, sun kara kaimi wajen yin kashedi dangane da daukar matakin soji.

Kamfanin dillacin labaran gwamnatin China ya ce, manyan kasashen yamma sun yi riga-malam masallaci wajen yanke hukunci dangane da wanda ya harba makamai masu guba a Syria, tun ma kafin masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya su kammala aikinsu.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce abin da zai biyo bayan kai harin, ba zai tsaya a Syria kadai ba, zai shafi kowace kasa a gabas ta tsakiya.

Karin bayani