Matsayin kasashen duniya a kan Syria

Amurka da kawayenta na duba yiwuwar amfani da karfin soji a kan Syria. Shin meye tunanin makwabtanta da sauran kasashen duniya a kan batun soma kaddamar da farmaki a kan Syria?

Makwabtan Syria:

Turkiya:

Gwamnatin Turkiya ta kasance daya daga cikin na gaba-gaba wajen sukar Shugaban Syria, Bashar al-Assad tun lokacin da aka soma yaki a kasar. A ranar Litinin, Ministan harkokin wajen Turkiyar, Ahmet Davutoglu ya shaidawa jaridar Miliyet ta kasar cewar a shirye Turkiya take ta hada hannu da kasashen duniya don daukar mataki a kan Syria ko da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya bai amince ba

Saudi Arabiya da Sauran kasashen Larabawa:

Image caption Ministan harkokin wajen Kuwait, Sheikh Muhammed Al Sabah

Sarakunan kasashen Larabawa su ne ke baiwa dakarun 'yan tawaye makamai da kuma tallafin kudi don yakar dakarun dake biyayya da Shugaba Assad. Saudi Arabiya ta kasance mai adawa da gwamnatin Syria tun shekaru masu yawa kuma tana kokarin kawar da Shugaba Assad, a yayinda rahotanni suka nuna cewar tsohon jakadan Saudi a Washington, Yarima Bandar bin Sultan ke kokarin samun goyon bayan kasashen duniya wajen taimakawa 'yan tawaye.

Isra'ila:

Duk da cewar da farko tana kokarin kaucewa sa baki a tashin hankalin, Isra'ila ta kai hare-hare a wurare uku a Syria a wannan shekarar, don hana mayakan Hezbollah na Lebanon shigar da makamansu. An kai luguden wuta daga Syria zuwa inda yahudawa suka mamaye a tuddan Golan inda Isra'ila ta maida martani.

Image caption Dakarun Isra'ila na sintiri a kan iyakarsu da Lebanon

A 'yan kwanakin nan, jami'an Isra'ila sun yi Allawadai a kan zargin amfani da makamai masu guba wanda ake yi wa dakarun Syria kuma sun ce za su goyi bayan amfani da matakin soji. Pirayi Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce " mun rike yatsunmu. Amma idan ya kama za mu saki yatsun"

Sai dai kuma jami'an Isra'ila sun kwana da sani a kan cewar idan kasashen yammacin duniya suka kaiwa Syria hari, za a iya maimaiata abinda ya faru a lokacin yakin tekun fasha a shekarar 1991, lokacin da Iraki ta kaiwa Tel Aviv hari da makami mai linzami don ta shigar da Isra'ila a cikin tashin hankalin sannan kuma kasashen Larabawa sun janye daga cikin yakin. Rahotanni su nuna cewar ana cikin sayar da abin kare fuska daga shakar iskar gas bisa fargabar daukar matakin soji a kan Syria.

Lebanon:

Tashin hankalin na Syria na kara shafar kasa Lebanon.

Ministan harkokin wajen Lebanon, Adana Mansour ya shaidawa gidan rediyon Lebanon a ranar Litinin cewar bai goyi bayan a kaiwa Syria hari ba, a cewarsa " bana tunanin matakin soji zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tsaron yankin".

Image caption Shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah

Hare-haren bama-bamai sau biyu sun hallaka mutane sittin a Lebanon a wannan watan kuma ana alakanta su da rikicin na Syria. Mayakan 'yan Shi'a na Hezbollah a Lebanon sun fito fili suna goyon bayan gwamnatin Syria kuma akwai rahotanni dake cewar wasu mabiya Sunnah suna yaki tare da 'yan tawaye. Bugu da kari, kasar na baiwa dubban 'yan gudun hijirar Syria mafaka.

Iran:

Iran ta kasance mai baiwa Syria goyon bayan a yankin tun kafin a soma wannan rikicin kuma ta nuna rashin amincewa ga duk wani yunkurin amfani da karfin soji.

A ranar Talata, Iran ta gargadi jami'an Majalisar Dinkin Duniya dake ziyara a Tehran cewar abin ba zai yi kyau ba idan har aka kaddamar da hari a kan Syria.

Kamfanin dillanci labarai na AFP ya ambato kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Abbas Araqchi na cewar 'yan tawayen Syria ne suka yi amfani da makamai masu guba.

Sauran kasashen duniya:

Amurka:

Bayan taka tsan-tsan a kan rahotannin farko game da amfani da makamai masu guba, Amurka a 'yan kwanakinnan ta zafafa matsayinta. Sakataren harkokin wajen kasar, John Kerry ya ce gwamnatin Syria ba za ta iya musanta zargin amfani da makamai masu guba ba.

Washington a kwanakin nan ta kara yawan dakarunta a gabashin tekun Mediterranean, abinda ya sa ake jita-jitar ta shirin kaddamar da kai hari. Masu sharhi na ganin cewar Amurka za ta kaddamar da hare-hare ne da makamai masu linzami ta cikin teku inda za ta kaiwa cibiyoyin sojin Syria hari.

Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaban Amurka, Barack Obama ya bayyana cewar amfani da makamai masu guba tamkar wuce gona da iri ne.

Birtaniya:

Birtaniya na shiri a kan amfani da matakin soji, kamar yadda kakakin Pirayi Minista ya bayyana, inda yace matakin da za a dauka zai yi daidai da abinda doka ta tanada da kuma irin yarjejeniyar da kasashen kawance suka amince.

A ranar Litinin, Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya shaidawa BBC cewar matsin lambar diplomasiyya baya aiki a Syria kuma " Amurka da sauran kasashe hadda Faransa sun bayyana a fili cewar ba za su bari a yi amfani da makamai masu guba tare da izza a karni na 21 ba".

Faransa:

Kwana guda bayan rahotannin hare-hare a kusa da Damascus, Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ya yi kira a "maida martanin soji" idan har aka tabbatar da amfani da makamai masu guba. Ya kara da cewar za a iya burus da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya idan har hakan ya kama.

Rasha:

Kasar Rasha ce babbar mai goyon bayan Shugaba Assad a duniya, kuma ta jadadda bukatar amfani da matakai na siyasa don warware rikicin.

Image caption Shugaba Vladmir Putin

Ta yi kakkausar suka a kan yiwuwar kasashen yammaci su kaiwa Syria farmaki, inda tace duk wani mataki da ya sabawa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai iya barazana ga kasashen Gabas ta Tsakiya da kuma na arewacin Afrika.

China:

China ta hade da Rasha don hana kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya dauki wani kwakkwaran mataki a kan Syria. Ta kuma soki duk wani yinkurin amfani da karfin soji a kan Syria.

Kamfannin dillancin labarai na gwamnatin China, Xinhua ya ce kasashen yammacin duniya sun yi gaggawar yanke hukunci a kan wanda ya yi amfani da makamai masu guba a Syria, tun kafin masu sa'ido na majalisar dinkin duniya su kamalla bincikensu.

Karin bayani