Majalisar Taraba ta ce Suntai bai koma aiki ba

Image caption Majalisa ba ta zauna ba

Majalisar dokokin jihar Taraba ta Nijeriya ta bayyana cewa har yanzu a saninta gwamman jihar, Mista Danbaba Danfulani Suntai bai koma kan mulkin ba, bayan da ya koma gida daga jinya a Amurka.

Hakan na faruwa ne kuwa duk da ikirarin da mukarabbansa ke yi na cewar ya koma bakin aikin.

A kan haka ne majalisar ta ce mukaddashin gwamnman jihar Alhaji Garba Umar ne ke rike da ragamar mulkin jihar.

Kakakin majalisar dokokin jihar ta Taraba ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, sai dai kuma wasu daga cikin yan majalisar na nuna adawa da wannan mataki.

Tun farko dai an shirya a yau Majalisar dokokin jahar ta Taraba za ta yi wani zama don duba bukatar gwamna Suntai dake kunshe a wasikar da ya ike mata cewar ya koma bakin aikinsa.

Sai dai hakan ba ta samu ba saboda rashin daidaiton da aka samu tsakanin yan majalisar dokokin.

Inda rahotanni suka nuna cewa an yi ta ganawar sirri tsakanin bangarori daban-daban game da batun.

Rahotanni dai sun ce an hana wasu daga cikin 'yan majalisar da suka ziyarci gidan gwamnan duba shi, ganinsa.

Har yanzu dai ba a ji daga shi kansa gwamnan Danbaba Suntai ba.

Karin bayani