Satar bayanai ta masarrafar Android

Image caption Apple ya ce fiye da kashi 93 na iPhones da iPads miliyan 600 da ya sayar suna da sabuwar masarrafar iOS 6.

Hukumomi a Amurka sun ce kashi 79 na satar bayanan da aka yi ta hanyar amfani da manhaja mai illa a wayoyin salula a shekarar 2012 sun faru ne ga wayoyin da ke amfani da masarrafar Android ta Google.

Wani shafin intanet da ke samar da bayanai kan yadda jama'a ke gudanar da rayuwarsu, mai suna Public Intelligence ne ya wallafa bayanan da ya samu daga ma'aikatar tsaron cikin gida ta Birtaniya da hukumar bincike ta Amurka wadanda suka tura wa rundunar 'yan sandan Amurka da likitocin da ke aikin gaggawa.

Bayanan sun nuna cewa manhajar Symbia da Nokia ke amfani da ita ita ce ta biyu kan satar bayanan da aka yi ta hanyar amfani da manhaja mai illa.

Ita kuwa manhajar iOS ta Apple tana da kashi 0.7 kan satar bayanan da aka yi ta hanyar amfani da manhaja mai illa.

Masarrafar Android ita ta fi kowacce masarrafar wayar salula tashe a duniya, kuma bayanan da aka fitar sun dora alhakin yawan satar bayanan ta da aka yi ta hanyar amfani da manhaja mai illa kan yawan masu amfani da ita da kuma tsarinta na barin kowa ya fige ta.

Sakonnin bogin da ake turawa ta manhajar wadanda ke sanyawa masu amfani da ita suna latsawa ba da saninsu ba su ne rabin abubuwan da ke janyo satar bayanan Android ta hanyar amfani da manhaja mai illa.

Bayanan sun kuma yadda shafukan intanet na bogi wadanda ke yin kama da Google's Play da "rootkits" ke bai wa mazambata damar gano lambobin sirri na shiga adireshin mutane.

Hukumomin sun ce kashi 44 cikin 100 na masu amfani da masarrafar Android suna yin amfani da tsohuwar masarrafa ne wadanda suka hada da 2.3.3 da 2.3.7, da ake yi wa lakabi Gingerbread wacce ta fito a shekarar 2011.

Wadannan masarrafa suna fuskantar barazana ta rashin tsaro, wadda aka kawar yayin da aka samar da sabbin masarafa.

Shi kuwa kamfanin Apple ya ce fiye da kashi 93 na iPhones da iPads miliyan 600 da ya sayar suna da masarrafar iOS 6, wacce ita ce sabuwar masarrafa.

A watan gobe ne ake sa ran kamfanin zai fitar da sabuwar masarrafa.

Karin bayani