'Yan gudun hijiran Najeriya a Diffa sun samu tallafi

Wasu mazauna birnin Maiduguri
Image caption Birnin Maiduguri ya kwashe sama da shekaru uku yana fama da tashin hankalin da ke da alaka da Boko Haram

Kungiyar agaji ta birnin Geneva, CICR ta baiwa 'yan gudun hijirar da suka tsere wa farmakin sojoji kan kungiyar da aka fi sani da Boko Haram, tallafin abinci.

Kimanin 'yan Najeriya 800 ne dake gudun hijira a jihar Diffa da wasu 'yan Nijar da suka koma gida, saboda suka amfana da tallafin abincin.

'Yan gudun hirar sun karbi tallafin shinkafa da wake da hatsi da kuma mai daga kungiyar.

Wannan ne karo na uku da kungiyar CICR ke baiwa 'yan gudun hijirar tallafi, kuma tana fatan ziyarar sauran yankunan da 'yan gudun hijiran suke a Nijar, domin ba su tallafi.