Saudiyya ta haramta cin zarafin masu aiki

Sarki Abdalla na Saudi Arabia
Image caption Sarki Abdalla na Saudi Arabia

Kasar Saudiyya ta kafa wata doka ta haramta cin zarafin masu aikin gida, ko da yake masu fafutuka na shakkar yadda za a aiwatar da dokar.

Dokar wacce kafar yada labaran kasar ta ce majalisar kasar ta amince da ita, ta tanadi zaman wakafi na shekara guda da tarar dala dubu13 ga wadanda suka karya ta.

Kafin yanzu, cin zarafin mata da kananan yara a gida, ya kasance wani abu ne da bai shafi hukuma ba, a karkashin doka a Saudiyya.

Masu fafutukar kare hakkin dan'adam sun yi maraba da dokar, sai dai sun ce akwai bukatar a bada horo ga alkalai da 'yan sanda, domin ganin sun fahimci sabuwar dokar.