An rushe majalisa da sunan Gwamna Suntai

Image caption Gwamnan Danbaba Danfulani Suntai

Gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai wanda ke fama da rashin lafiya, ya rushe majalisar zartarwa ta jihar tare da sauke duka masu bashi shawara.

Mataimaki na musamman ga gwamnan, Mista Sylvanus Yakubu wanda ya sanar da haka, ya ce gwamnan kuma ya nada sabon Sakataren Gwamnatin jihar da kuma Shugaban Ma'aikatan fadar gwamnati.

Ita dai Majalisar dokokin jihar Taraba ta bayyana cewa har yanzu a saninta gwamman jihar, Mista Danbaba Danfulani Suntai bai koma kan mulki ba, bayan da ya koma gida daga jinya a Amurka.

A kan haka ne majalisar ta ce mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar ne ke rike da ragamar mulkin jihar.

Gwamna Danbaba Suntai ya yi hadari a jirgin sama abinda ya tilasta shi shafe kimanin watanni goma yana jinya a kasashen Jamus da Amurka kafin a dawo da shi Najeriya a ranar Lahadi amma cikin yanayi rashin lafiya.

Karin bayani