Birtaniya za ta gabatar da kuduri kan Syria

Image caption Cameron da Obama na shiri a kan Syria

Birtaniya za ta gabatar wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wani kuduri a ranar Laraba a kan neman umurnin daukar matakan kare fararen hula a Syria.

Za a gabatar da kudurin ne a taron da wakilai biyar na dundundun na kwamitin tsaron za su yi kamar yadda Pirayi Ministan Birtaniya, David Cameron ya bayyana a shafin Twitter.

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan Mista Cameron ya tattauna da Shugaba Obama ta wayar tarho inda shugabannin biyu suka zargi gwamnatin Syria da alhakin kai hari da makami mai guba.

Tun da farko, tawagar binciken makamai ta Majalisar Dinkin Duniya ta koma aikin gano zargin kai hari da makami mai guba a Syria a ranar 21 ga watan Agusta.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya yi kira ga kwamitin ya dauki hukunci.

Mista Ban yace" kwamitin dake da muradin gannin an samu zaman lafiya a fadin duniya ba zai kawar da kai ba".

Karin bayani