Amurka na rokon afuwa ga Koriya ta Arewa

Image caption Mr. Bae mai wa'azi mishan ne kuma yana da wani kanfanin yawon bude ido a kasar.

Amurka za ta aika da wani babban jami'inta zuwa Koriya ta Arewa domin rokon kasar ta saki wani ba'amurke da ke daure a can.

Ma'aikatar Harkokin wajen Amurka ta ce Robert King, Manzon Amurka na musamman kan kare hakkoki zai isa birnin Pyongyang ranar Jumua, inda zai roki a yi wa Kanneth Bae mai shekaru 45 afuwa bisa dalilan jinkai.

An daure Bae wanda Ba'amurke ne dan asalin Koriya daurin shekaru 15 tare da aiki mai wahala a watan Mayu; bayan samun shi da laifin ingiza wasu 'yan kasar su yi yunkurin kifar da gwamnatin Koriyar.

Iyalinsa sun ce ya ba ya da lafiya kwarai da gaske inda har an dauke daga wani sansani gwale-gwale zuwa wani asibiti saboda yana fama da ciwon suga da kuma kumburin zuciya.

Magiya

''Mu na cikin matukar damuwa game da yanayin lafiyar Kenneth Bae. Muna rokon gwamnatin Koriya ta Arewa da ta yi wa Mr. Bae afuwa ta musamman kana ta bar shi ya dawo gida tare da Ambassador King'' Inji wata sanarwa da fadar White House ta fitar.

Koriya ta Arewa dai ta kama 'yan kasar Amurka da dama a 'yan shekarun nan ciki har da 'yan jarida da kiristoci da take zargi da mayar da wasu 'yan kasar kiristoci.

Karin bayani