Ambaliyar ruwa a birnin Bamako

Ambaliyar ruwa a Bamako
Image caption Ambaliyar ruwa ba sabon abu bane a birnin na Bamako

Akalla mutane 24 ne suka mutu a ambaliyar ruwa, sanadiyyar tafka ruwan sama da aka yi a Bamako babban birnin Mali, a cewar jami'an gwamnati.

Wani wanda ya shaida lamarin ya ce ruwan ya yi awon gaba da wasu motoci kirar tasi dake dauke da fasinjoji.

Yayin da wasu kuma suka mutu, saboda gidajensu na kasa da suka ruguje.

Wannan ce ambaliya mafi muni cikin shekarun da suka wuce, a birnin dake gabar kogin kwara, kuma wasu daga gidajen da abin ya shafa ba a gina su bisa ka'ida ba.