Dubban jama'a sun tsere wa Seleka

'Yan tawayen Seleka
Image caption Faransa ta yi gargadin cewa Afrika ta tsakiya za ta iya koma wa kamar Somalia

Dubban fararen hula ne suka tsere zuwa babban filin jiragen sama na Afrika ta Tsakiya, domin gujewa tashin hankali.

Jama'ar sun mamaye titin jiragen na wani dan lokaci, abin da ya hana wasu jirage sauka a filin jirgin.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce, mazauna wata unguwa dake kusa da filin jirgin, sun fara barin gidajensu ne, a lokacin da 'yan tawayen Seleka suka fara harbi a unguwar.

Jamhuriyar ta Afrika ta Tsakiya ta shiga rudani, tun bayan da 'yan tawayen suka tumbuke shugaba Francois Bozize a watan Maris.

A ranar Talatar da ta gabata ne, shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sa hannu a lamarin.