Rwanda ta la'anci harba ma ta makamin roka

'yan gudun hijirar Rwanda
Image caption 'yan gudun hijirar Rwanda

Gwamnatin Rwanda ta la'anci kashe wata mata 'yar kasarta, sakamakon makamin roka da ya fadi kusa da ita, a kan iyaka da jamhuriyar Dimokradiyyar Congo .

Rwandar ta bayyana harba rokar da cewa takalar fada ne.

Haka nan an bayar da rahoton cewar yaronta ya samu rauni a lamarin da ya faru a garin Rubavu na kan iyaka.

Rwanda dai ta zargi sojojin Congo da harba makamin.

Ita dai gwamnatin Congon, a birnin Kinshasa ta musanta harba rokokin , tana mai dora laifin a kan 'yan tawayen M23.