Ban Ki-Moon na dakon rahoto kan Syria

Image caption Obama da Cameron na son a yaki da Syria

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya ce yana sa ran karbar rahoton masu binciken makamai da ke aiki a Syria a ranar Asabar mai zuwa.

Shugaba Obama na Amurka ya ce har yanzu bai yanke shawara ba tukuna, a kan wani shiri na kaddamar da ramuwar gayya a kan Syria.

Amma ya jaddada cewar dakarun gwamnatin Syria ne ke da alhakin kai hare-hare da makamai masu guba a kewayen birnin Damascus.

Mista Obama ya ce duk wani mataki da za'a dauka zai kasance na aikewa da wata alama mai karfi ga Syria, domin a hana ta amfani da irin wadannan makamai masu guba a nan gaba.

Tuni dai Rasha wacce itace babbar kawa ga Syria ta tare wani yunkuri da Birtaniya ke jagoranta a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya na ganin an dauki matakan kare fararen hula.

Ministan harkokin wajen Rashan ya ce majalisar dinkin duniya ba za ta iya gabatar da shawarar daukar mataki ba a kan Syria, kafin masu bincike su kammala aikinsu.

'Fargabar yaki'

A babban birnin Damascus na Syria yiwuwar daukar matakin soji na ci gaba da janyo fargaba.

An ruwaito cewa manyan Komandojin soji sun bada umarnin a kwashe dukkanin jami'ai daga mahimman cibiyoyi a wuraren babban birninn Kasar.

Ana kuma samu dogayen layukan motoci makare da akwatuna suna jiran su tsallaka cikin Kasar Labanon.

Karin bayani