Amurka za ta yi gaba-gadi kan Syria

Image caption Amurka na ta hankoron kai farmaki Syria

Kasar Amurka ta bada haske cewa ita fa za ta iya aiwatar da amfani da karfin soji kan Syria ita kadai.

Wadannan kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Birtaniya ta gaza samun kuri'un da zai bata damar sa hannu a kai farmakin a Syria.

Jim kadan bayan an kada kuri'ar ne Sakataren tsaro na Birtaniya Phillip Hammond ya ce dakarun Birtaniya ba za su yi amfani da karfin soji ba a Syria.

A Washington kuwa fadar White House ta ce ta ga sakamakon kada kuri'ar da aka yi a Birtaniya kuma za ta ci gaba da tuntubar Birtaniyar.

Amma a cewar Fadar matakin da shugaba Obama yake dauka za kasance ne ya yi dai-dai da ra'ayin kasar Amurka.

Karin bayani