Kayan itace da ke rage kamuwa da ciwon suga

Kwayoyin ciwon suga
Bayanan hoto,

Cutar na hana jiki sarrafa suga kamar yadda ya kamata

Wani sabon nazari na nuna cewa cin kayan marmari a matsayin abinci, na rage hatsarin kamuwa da ciwon suga nau'i na biyu.

Bayan gudanar da bincike kan mutane kusan dubu 200, masana a Amurka sun gano cewa mutanen dake cin kayan marmari, kamar su inibi da tufa da blueberries, za su iya rage kamuwa da cutar da kusan kashi daya cikin hudu.

Amma wasu kayan marmarin ba sa sauya komai, kamar su kankana da strawberries.

Masanan sun kuma gano cewa shan lemon da aka yi da kayan marmari, na kara hatsarin kamuwa da ciwon sugan nau'i na biyu.