'Yan gudun hijira a Kamaru za su yi rijista

Image caption 'Yan Najeriya 'yan gudun hijira za su yi rigista

Gwamnan lardin arewa mai nisa a Kamaru, Awa Fonka Augustine, ya yi kira ga 'yan gudun hijira 'yan asalin Najeriya da su gaggauta yin rajista domin a tantance su.

Wannan dai a cewar hukumomin Kamaru zai bawa 'yan gudun hijirar damar cin moriyar tallafi daga wurin gwamnatin kasar da kuma Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira.

Tun lokacin da Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya dokar ta baci a wasu jihohi 3 na arewacin kasar ,jama'a dama suka fice don neman mafaka a Kamaru.

Akalla dai 'yan gudun hijirar da suka kwarara zuwa Kamaru sun doshi mutane dubu biyu.

Karin bayani