Syria ta yi maraba da matsayin Birtaniya

Shugaban kasar Syria Bashar Al'assad
Image caption Amma Mr. Cameron ya amince Birtaniya ba za ta dauki matakin soji a kan Syria ba, saboda kuri'ar majalisar.

Wakilin BBC a Syria ya ce kasar ta yi maraba da kayen da gwamnatin Birtaniya ta sha, a hannun 'yan majalisa, a kuri'ar da aka kada.

A Rasha shugaban kasar Vladimir Putin ya ce kuri'ar Birtaniya na nuni da cewa, mutane sun fara fahimtar hatsarin dake tattare da daukar matakin soji a kan Syria.

Amma kungiyar 'yan adawa dake gudun hijira ta 'Syrian national Coalition' ta ce, ta ji bakin ciki game da yadda kuri'ar ta kaya.

Firai ministan Birtaniya David Cameron ya ce zai ci gaba da yunkurin ganin an dauki mataki a kan gwamnatin Syria.