Kerry:An kashe mutane 1,429 a harin Syria

Image caption John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce dakarun gwamnatin Syria sun kashe mutane 1,429 a harin da suka kai da makamai masu guba a Damascus a makon da ya gabata.

Mista Kerry ya ce daga cikin wadanda aka kashe hadda yara 426.

Ya bayyana cewar rahoton jami'an leken asiri ya nuna cewar Shugaba Assad ya yi amfani da makamai masu guba a Syria.

A cewar Kerry, Amurka ba za ta maimaita abinda ya faru a Iraki game da bayyanan sirri a kan Syria.

'Binciken makamai'

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya ce sufetocin makamai sun kamalla daukar shaidu a kan zargin amfani da makamai masu guba a Damascus.

Kakakin Martin Nesirky, ya ce bai san tsawon lokacin da za a shafe ba kafin a kamalla gwaje-gwajen shaidun da ake dasu sannan ya bada sakamakon.

Ya bayyana haka ne jim kadan bayan da Sakatare Janar, Ban Ki-moon ya gana da wakilan kasashe biyar mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Karin bayani