An nuna rashin gamsuwa kan hukuncin fyade a Indiya

Shari'ar aikata fyade a Indiya
Image caption Shari'ar aikata fyade a Indiya

A India iyalan dalibar nan da gungun wasu karti suka yi wa mummunan fyade har ta mutu a birnin Delhi cikin watan Disamba sun ce, ba su gamsu ba da irin hukuncin da aka yanke wa saurayin da aka samu da laifin aikata fyaden ba.

Saurayin da aka samu da laifin aikata fyaden, mai shekaru goma sha bakwai a lokacin da ya aikata laifin, yanzu an yanke masa hukuncin zaman shekaru uku a gidan tsare kangararrun yara.

Asha Singh , mahaifiyar dalibar da aka kashe sakamakon fyaden, ta ce sun yi takaici kan wannan hukunci, wanda suke ganin an yi sassauci kwarai.

Asha ta ce abin da suka yi fatan gani shi ne a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.