Masu bincike sun bar Syria

Masu bincike na daukar samfurin makami mai guba a Damascus
Image caption Masu binciken yiwuwar amfani da makamai masu guba na Majlisar Dinkin Duniya sun gama aikinsu a Syria.

Masu binciken makamai masu guba na Majalisar Dinkin Duniya da suka gudanar da aikin binciken zargin amfani da makamai masu guba a wajen birnin Damascus sun bar kasar ta Syria.

Ana dai sa ran masu binciken makaman zasu mikawa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya sakamakon binciken da suka gudanar bayan anyi gwajin shaidun da suka tattara a dakunan gwajin kimiyya.

Akwai rahotanni da ke cewa dakarun gwamnatin Syria na kwashe kayayyakin su zuwa yankin fararen hula, da suka hadar da makarantu da masallatai, saboda tunanin mai yiwuwa Amurka za ta kai hari.

Wakilin BBC a Syria ya ce mazauna yankin Damascus na tara kayan abinci a gidajensu, ya yin da wasu ke barin kasar baki daya.

Karin bayani