An sallamo Mandela daga asibiti

Image caption Mandela na kara samun sauki

An sallamo tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela daga asibiti.

Nelson Mandela wanda yake kwance a asibiti rai kwa-kwai mutu kwa-kwai tun watan Yuni an koma da shi gidansa dake Johannesburg.

Sai dai kawo yanzu babu wata sanarwa daga gwamnati kan sallamar tsohon shugaban daga asibiti.

Tsawon lokacin da Mandela ya yi a asibiti ya jawo damuwa a Afrika ta kudu da ma kasashen ketare.

Wannan labarin dai zai zama abin farin ciki ga 'yan kasar.

Karin bayani