Syria: Obama ya yi jawabi a kan kai hari

Shugaba Obama ya gudanar da jawabi akan batun Syria yana cewa, zasu ɗau mataki a kan Syria a duk lokacin da suke so, amma yace, zai nemi amincewar majalisar dokokin kasar.

Obama yace, duk da cewar zai iya daukar matakin soja a kan Syria ba tare da izinin majalisar dokoki ba, amma zai nemi amincewarsu domin su wakilan jama'a ne.

Obama yace, abinda ya faru a Syria wata babbar barazana ce ga ƙawayenta dake maƙwabtaka da Syria.

Shugaban na Amurka yace, dakarun Amurka a shirye suke kuma za su iya kai hari a Syria ko yaushe suke so.

Obama ya kammala jawabinsa da cewa, Amurka zata ci gaba da tallafawa 'yan tawayen Syria.