An gurfanar da dan wani Shugaban kasa a Kotu

Image caption Dino Bouterse ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa

Dan shugaban Surinam ya bayyana a gaban wata kotu a Amurka, inda ake zargin sa da safarar miyagun kwayoyi da makamai.

Dino Bouterse yaki amsa laifin sa a gabatan kotun Tarayya da ke New York.

Mr. Bouterse wanda ada shi ne shugaban sashen yaki da ta'addanci a Surinam, an kama shi ne ranar Alhamis a Panama, inda aka mika shi ga jami'an Amurka.

A baya ma wata kotu a kasar Holland ta yanke wa mahaifin Dino, wato shugaba Desi Bourterse hukunci, saboda samun sa da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Karin bayani