Artabu tsakanin sojoji da Ombatse a Akwanga

Umaru Tanko Almakura, Gwamnan Jihar Nasarawa, Najeriya
Image caption Umaru Tanko Almakura, Gwamnan Jihar Nasarawa, Najeriya

Rahotanni daga garin AKwanga dake jihar Nasarawa a Nijeriya na cewa an kashe mutane akalla takwas da suka hada da sojoji uku da 'yan kungiyar nan da ake kira Ombatse mai dauke da makamai dake bin addinin gargajiya su biyar.

Lamarin dai ya faru ne dazu da rana a wani wurin binciken matafiya.

Hukumomin 'yan sanda a jihar ta Nassarawa dai sun tabbatar da kashe wasu da suke zargin 'yan kungiyar asirin ta Ombatse ta 'yan kabilar Eggon.

Ko a kwanakin baya dai an samu rikici tsakanin 'yan kabilar ta Eggon da Alago, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da kona gidaje a karamar hukumar Obi.

To amma wannan rikici na baya baya ya faru ne tsakanin 'yan kungiyar ta Ombatse da jami'an tsaro a kusa da garin Akwanga.