Boko Haram sun kashe mutane 24 a Borno

Image caption An yiwa 'yan kungiyar sa kai kwantan bauna

Wasu da ake zargin 'yan Kungiyar Boko Haram ne a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun kashe akalla 'yan kungiyar sa kai ta matasa da ke aikin samar da tsaro guda ashirin da hudu.

Haka kuma wasu 'yan sa kan talatin da hudu ba a ji duriyar su ba bayan harin da aka kai musu a jihar Borno ranar juma'ar da ta gabata.

Jami'ai sun ce, 'yan bindigar sanye da kayan sojin sun yi wa matasan kusan dari kwantan bauna a wani daji.

Rahotanni sun ce, rundunar sojan Najeriya na bada goyon bayan kafa kungiyar sa kai ta matasa da ke aikin samar da tsaro domin taimakawa wajen kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi.

Karin bayani