Ethiopia: An yi zanga-zangar ƙyamar tsarin ra'ayin addini

Image caption Praministan Ethiopia, Hailemariam Desalegn

Dubban mutane ne suka halarci wani babban gangamin nuna kyamar tsatsauran ra'ayin addini a Ethiopia.

An dai tsaurara matakan tsaro a dandalin da aka yi gangamin dake tsakiyar birnin Addis Ababa, kuma an hana motoci shiga wurin gangamin.

Cikin watan da ya gabata ne dai ɗaruruwan musulmi suka yi zanga-zangar kiran gwamnati ta daina yin katsalandan a sha'anin da ya shafi addini.

Sun kuma nemi a sako shugabannin musulmi da ake tsare da su.

Musulmi dai sun kai kusan kashi arba'in cikin ɗari na al'ummar ƙasar ta Habasha.