An sallamo Mandela daga asibiti

Tsohon shugaban kasar Afurka ta kudu Nelson Mandela
Image caption Mr Mandela ya dade ya na fama da cutar huhu, inda al'umar Afurka ta kudu da ma duniya ke damuwa akan dadewarsa a asibiti

A sanarwar da gwamnatin Afurka ta kudu ta watsa a shafin ta na internet, ta ce har yanzu Mr Mandela na cikin mawuyacin hali, sai dai a wasu lokutan ya na samun ahuwar jikin na sa.

Amma likitocin da suke kula da shi sun amince cewa, zai ci gaba da karbar taimakon da ake ba shi a asibiti anan gidan na sa da ke Johannesburg.

An kuma yi gyara a gidan na sa, domin ba shi taimakon da ake masa a asibiti.

Mr Mandela dan shekaru casa'in da biyar a duniya, wanda ya kasance shugaba bakar fata na farko a Afurka ta kudu ya dade a sibiti tun watan Yunin da ya gabata, inda yake fama da cutar huhu.

A ranar asabar hukumomin Afurka ta kudu suka musanta rahotannin da ke cewa an sallamo Mr Mandela daga asibiti.