Za mu tabbatar an hukunta Syria —Faransa

Jean-Marc Ayrault
Image caption Piraministan Faransa, Jean-Marc Ayrault

Praministan Faransa, Jean-Marc Ayrault, ya gaya wa shugabannin majalisar dokokin kasar cewa, bai kamata a yi shiru ba, bayan harin makamai masu gubar da aka kai a Syria.

Mr Ayrault ya bayyana hakan ne yayin da aka gabatar wa 'yan majalisar shaidun da ke kamsasa ikirarin cewa, dakarun shugaba Assad ne suka kai harin.

Tun farko gwamnatin Faransar ta fitar da rahoto akan harin ranar 21 ga watan Agusta, wanda ya ce binciken fasahar da aka gudanar kan makaman rokar da aka harba wajan ya nuna an yi amfani da su ne a matsayin makamai masu guba.

Rahoton ya ce gwamnatin Syria ta yi ruwan bama-bamai a wajen bayan harin domin a lalata duk wata shaidar da za'a iya samu a kuma samu jinkirin isar sufetocin Majalisar dinkin duniya masu binciken makamai.

Sai dai rahoton ya bayyana cewa mutanen da lamarin ya shafa ba su kai ko da kusa da wadanda rahotannin sirrin Amurka suka ce ya shafa ba, yana mai cewa akalla mutane 281 suka mutu sakamakon harin.

Sai dai shugaban Syriar, Bashar al- Assad ya yi hannunka mai sanda ga Faransar, game da daukar duk wani mataki a kan kasarsa.

Karin bayani