Mandela ya kwana daya a gidansa

Image caption Mandela ya na gidansa na Johannesburg

Tsohon shugaban Afrika ta kudu Nelson Mandela ya yi kwana na farko a gidan sa da ke Johanesburg bayan sallamar sa daga asibiti sakamakon shafe kusan watanni uku yana jinyar cutar huhu.

Iyalansa sun bayyana farin cikin su saboda dawowar tasa gida, sai dai gwamnatin kasar ta ce har yanzu jikin nasa dai akwai saura, kuma zai cigaba da karbar kulawar likitoci kamar yadda ake masa a asibiti.

Wata mazauniyar Pretoria ta bayyana farin cikin ta dangane da sallamar tasa inda take cewa sun ji da di kuma labari ne mai da di da su ka ji cewa ya warware.

'Yan kasar dai sun sha yin aduu'oi don neman samawa tsohon shugaban Afrika ta kudun lafiya.

Karin bayani