An kama dan majalisa kan rikici a Nijar

Wasu jami'an tsaro a Nijar
Image caption Wasu jami'an tsaro a Nijar

Jami'an tsaro a jamhuriyar Nijar sun kama wani dan majalisa, Jafar Muminu khalilou bisa zarginsa da hannu a fito-na-fiton da mazauna garin Gudel su ka yi da jami'an tsaro.

'Yan sanda sun kama dan majalisar na jam'iyyar Model Lumana ne a ranar Litinin, bayan jami'an tsaro 26 da fararen hula 16 sun jikkata a tashin hankalin na ranar Lahadi.

Mazauna Gudel sun koka a kan matakan tsaron da hukumomi suka dauka, a kan hanyar zuwa garin daga birnin Yamai.

Hukumomin sun dauki matakan ne sakamakon hare-haren ta'addancin da Nijar ta fuskanta, musamman ganin cewa ofisoshin jakadancin kasashe da dama na kan wannan hanyar.