Kungiyar Larabawa ta zargi Syria

Image caption Kungiyar Larabawa na bukatar a ladabtar da Syria

Kungiyar kasashen larabawa ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen duniya da su dauki matakan ladabtarwa a kan Syria.

A yayin wani taron ministocin harkokin waje a Alkhahira, kungiyar ta kuma zargi gwamnatin Syria da kai hari da makamai masu guba a watan da ya gabata.

Mai magana da yawun kungiyar kasashen larabawan, Nassif Hitti ya shaidawa manema labarai cewa sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kasashen duniya da su duba nauyin da ya rataya akansu bisa tsarin dokokin kasa da kasa dan daukar matakin da ya dace a kan Syria.

A Faransa, Firaminista Jean Marc Ayrault zai gana da shugabannin majalisar dokoki dan shaida musu yiwuwar daukar mataki a kan Syria.

Karin bayani