Tarin fuka ya samo asali daga Afrika

Kwayoyin cutar tarin fuka ko TB
Image caption Mataki na gaba a nazarin shi ne gano yadda cutar kan boye kanta na wani lokaci, sannan ta bayyana kanta

Wani nazari da masana na kasashen waje suka yi, ya nuna cewa tarin fuka ya samo asali ne, daga wasu mafarauta a Afrika shekaru 70,000 da suka wuce.

Nazarin wanda aka wallafa a mujallar 'Nature Genetics' ya nuna dangantaka mai karfi tsakanin tarihin bunkasar dan Adam da cutar.

Tarin fuka ko tarin TB na kashe akalla mutane sama da miliyan daya duk shekara.

Cutar dai ta kan dauki tsawon shekaru a jikin dan Adam, kafin ta bayyana.

Nazarin baya

Binciken da aka yi a baya na nuna cewa cutar tarin fuka da mutane ke fama da ita, ta samo asali ne shekaru 10,000 da suka wuce a Afrika.

A lokacin da al'umma ke bunkasa kuma ake samun daukakar aikin noma.

Manazartan sun yi amfani da bayanan yanayin kasa da na kwayoyin halitta daga tarin TB 259 da aka samu, kuma suka gina tarihin cutar, tare da kwatanta shi da asalin bil'adam a nahiyar.

Farfesa Sebastian Gagneux na cibiyar binciken cututtuka a gurare masu zafi ta Switzerland ya ce "Mun gano cewa tushen tarin fuka da na dan Adam sun samo asali a Afrika, shekaru 60,000 sama da yadda da fari aka yi tsammani. "

A cewar farfesan daga bisani ne cutar ta yadu daga dan Adam zuwa dabbobi.