Majalisar Kenya na muhawara kan ICC

Mataimakin shugaban Kenya, William Ruto
Image caption Shugaba Kenyatta ma zai gurfana a gaban kotun a watan Nuwamba bisa tuhuma irin ta Mr. Ruto

Majalisar dokokin Kenya ta kira wani zama na musamman, domin tattauna batun janyewa daga kasashen da suka sa hannu a kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya.

Akwai yiwuwar majalisar ta amince da janyewar kasar, abin da zai sa ta zama kasa ta farko data balle daga kasashen da suka rattaba hannu kan kotun ta ICC.

A makon gobe ne mataimakin shugaban kasar William Ruto, zai gurfana a gaban kotun kan tuhume-tuhumen da suka shafi zargin cin mutuncin al'umma.

Kotun ta ICC ta ce za ta ci gaba da sauraron karar, ko da kuwa Kenya ta fice.