Takun saka a PDP ya kai gaban kuliya

Image caption Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

Rahotannin da kafafen yada labaran Najeriya suka wallafa na nuna cewar bangaren 'sabuwar' PDP ya kai kara gaban babbar kotu a Lagos don hana bangaren shugabancin Alhaji Bamanga Tukur bayyana kansa a matsayin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta PDP.

Wata Sanarwa da Sakatare Janar na 'sabuwar' PDP da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da wasu gwamnoni ke marawa baya, ta ce sun shigar da kara gaban kuliya ne don Alhaji Bamanga Tukur da bangaren shugabancinsa ba sune hallatattun 'yan kwamitin gudanarwar jam'iyyar ba.

Kwamitin gudanarwar 'sabuwar PDP' su ne Alhaji Kawu Baraje, Dr. Sam Sam Jaja, Prince Olagunsoye Oyinlola sai kuma daya bangaren wanda ya kunshi Alhaji Bamanga Tukur, Prince Uche Secondus, Mrs. Kema Chikwe da kuma Olisah Metuh .

A karshen mako ne jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta dare gida biyu inda tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar da wasu gwamnoni bakwai suka balle daga bangaren da suka kira 'tsohuwar' PDP.

Rahotanni daga wasu kafafen yada labarai a Najeriya sun nuna cewar 'yan majalisar dattijai kusan 22 sun hade da bangaren shugabancin Kawu Baraje na jam'iyyar ta PDP.

Daga cikin Sanatocin harda Bello Hayatu Gwarzo da Mohammed Ali Ndume da Abdulahi Adamu da kuma Abubakar Bukola Saraki.

Karin bayani