Salva Kiir zai ziyarci jamhuriyar Sudan

Shugaba El-Bashir da takwaransa Salva Kiir
Image caption Ziyarar ta biyo bayan amsa goron gayyata daga Shugaba Umar Hassan El-Bashir

Wata tawagar Sudan ta Kudu a karkashin jagorancin Shugaban kasar Salva Kiir, za ta fara wata ziyarar aiki ta kwana uku a kasar Sudan.

Shugabannin kasashen biyu za su jagoranci tattaunawa a kan huldar danganta tsakanin kasashensu.

Za kuma su duba batutuwan da suka shafi harkar mai da ma'adinai da masana'antu da harkokin kudi da cinikayya da saka jari da tsaro da harkokin cikin gida wadanda suka alakanta kasashen biyu.

Har ila yau kuma tattaunawar za ta tabo inda aka kwana, wajen aiwatar da yarjejeniyoyin hadin-gwiwa da aka kulla tsakanin kasashen biyu a bara a dukkan fannonin.