Syria: Isra'ila ta gwada makami mai linzami

Image caption Isra'ila ta tauna tsakuwa don aya taji tsoro

Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta tabbatar cewa, ta yi gwajin makami mai linzami a yankin tekun Mediterranean, a wani bangare na atisayen hadin gwiwa da Amurka.

Wani babban jami'in Isra'ila ya shaidawa BBC cewar sun harba makamin mai linzami mai suna F-15 a daga cikin jirgin sama.

Hakan ya faru yayin da can a Washington ake nuna cewa, akwai yiwuwar shugaba Obama na shirin daukar gagarumin matakin soja a kan Syria, saboda zargin ta yi amfani da makamai masu guba, ba wai hare-hare nan da can ba, wadanda aka fito fili aka bayyana tun farko.

Wakilin BBC a birnin Kudus ya ce gwajin wata alama ce a kan cewar Isra'ila na shirin kota kwana na daukar matakin ramuwar gayya idan Amurka ta kaddamar da hari a kan Syria, sannan ita kuma Isra'ilar ta maida martani kan Isra'ilar.

Itama hukumar leken asirin kasar Jamus, BND, ta ce ta yi ammanar cewa gwamnatin Syria ce takai harin da aka kai da iska mai guba a wajen birnin Damascus.

Karin bayani