Syria: John Boehner ya goyi bayan Obama

Image caption John Boehner ya ce Amurka ta ja kunnen Syria

Kakakin majalisar wakilan Amurka, John Boehner, wanda dan jam'iyyar Republican ne ya ce ya goyi bayan kiran da shugaba Obama ya yi na daukar matakin soji a kan Syria.

Da yake magana bayan ganawarsa da Mista Obama, Mista Boehner ya ce Amurka ta ja kunnen gwamnatin Syria da cewa ba za a yadda da amfani da makamai masu gubar da take yi ba.

Wakilin BBC a Washington ya ce goyon bayan da Mista Boehner wani babban ci gaba ne ga Mista Obama, ko da yake wannan ba yana nufin yin nasara ba ne idan majalisar dokokin ta tabka mahawara kan shiga Syria a makon gobe.

Tun da farko shugaba Obama ya ce yana da tabbacin samun goyon bayaa kan abin da ya kira dan takaitaccen mataki a kan Syria.

Ya ce, ''Wannan wani takaitaccen mataki ne wanda ba zai wuce kima ba da zai aike da sako ba wai kawai ga gwamnatin Assad ba har ma da kasashen da ke sha'awar daukar irin wannan mataki cewa akwai abin da zai biyo baya''.

Karin bayani