Martabar duniya na fuskantar zubewa - Obama

Image caption Shugaba Barack Obama

Shugaba Obama ya ce ba wai mutuncinsa ne ke neman zubewa game da yin amfani da makamai masu guba a Syria ba, kasashen duniya ne baki daya.

A wajen wani taron manema labarai a Sweden, Mr Obama ya ce bas hi ne ya shata layin da ba za a ketara ba a kan makamai masu guba, duniya ce ta yi, ta hanyar haramta yin amfani da irin wadannan makamai.

Haka nan shi ma Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce rashin daukar mataki kan Syria na tattare da hadari mafi girma fiye da daukar matakin soji kan gwamnatin Shugaba Assad.

Yana dai magana ne a gaban kwamitin majalisar dokokin da ke duba bukatar shugaba Obama na daukar matakin soji.

A bangare guda kuma kasashe 4 makwabtan Syria, sun bayyana takaicinsu da rashin jin dadi da rashin ba su taimako game da ‘yan gudun hijira miliyan 2 da suka tsere daga Syriar zuwa kasashensu.

Karin bayani