Ariel Castro ya rataye kansa a kurkuku

Image caption Castro dai ya amsa aikata duka laifukka 937 da ake zarginsa da aikatawa ciki har da fyade sau tari.

Hukumomin gidan Yari a jihar Ohio ta Amurka sun ce an samu Ariel Castro, rataye a dakin da ake tsare da shi.

Castro shi ne mutumin da ya sace wasu mata uku kana ya tsare su kusan tsawo shekaru goma yana lalata da su.

An tsare Catsro ne a wani wuri na daban shi kadai saboda hadarin da yake da shi, hukumar ta ce ana zuwa rangadinsa kowadanne mintoci talatin.

Ma'aikatan lafiya na gidan yarin sun yi kokarin farfado da shi, amma abin ya faskara daga bisani kuma aka ruga dashi zuwa asibiti inda aka tabbatar da ya mutu.

A watan Agusta ne aka daure Mr. Castro daurin shekaru dubu daya da doriya, saboda sace matan uku.

Karin bayani