Majalisar Amurka ta goyi bayan kai hari Syria

Image caption An amince da daftarin ne bayan John Kerry ya bayyana gaban kwamitin majalisar mai kula da harkokin waje.

Kwamitin majalisar dattawan Amurka mai kula da harkokin waje, ya amince da wani daftari wanda idan aka rattaba masa hannu, zai ba da izinin amfani da karfin soji a kan Syria.

Kudurin wanda za a jefa kuri'a a kansa a mako mai zuwa, zai ba Shugaba Barack Obama izinin daukar ''takaitaccen'' matakin sojin da ba zai wuce kwanaki 60 ba.

Ko da yake za a iya kara tsawon wa'adin da kwanaki 30, idan majalisun sun amince, sai dai kudurin ya hana amfani da kowane irin karfin soji ta kasa a Syrian.

Tuni dai Kakakin majalisar wakilan kasar, John Boehner ya mara wa shawarar Obama ta kaiwa Syria hari.

Karin bayani