'Yan Syria na sadaukar da kansu a kan Assad

Image caption Matasan dai na son tunkarar 'yan tawaye ne da ake jin za su iya kai wa shugaba hari.

Wasu fareren hula a babban birnin Syria, wato Damascus sun fara dinka kakin soji suna kuma karbar bindigogi daga gwamnati domin kare Shugaba Assad.

Hotunan tallabijin daga birnin na Damascus sun kuma nuna wasu matasa maza da mata, sun taru domin yiwa wasu cibiyoyi soji da ake sa ran Amurka za ta kai wa hari garkuwa da jikinsu.

Wasunsu na dauke da alluna masu sakonnin da ke cewa ''Sai dai bayan ranmu."

''Kasashen Iran da Rasha da kuma Kungiyar Hizbullah, duk suna tare da mu kuma za mu ci nasara'' Inji wata matashiya da ta zanta da wakilin BBC Jeremy Bowen.

Karin bayani