Zazzabin cizon sauro ya munana a Chadi

Mutane na fama da zazzabin cizon sauro
Image caption Mutane na fama da zazzabin cizon sauro

Ma'aikatan lafiya sun yi kashedi game da karuwar mutane masu dimbin yawa dake kamuwa da zazzabin cizon sauro, a yankin kudu maso gabashin kasar Chadi.

Kungiyar agajin likitoci ta Medicins Sans Frontiers, ta ce adadin masu fama da zazzabin cizon sauron a yankin Salamat ya haura zuwa dubu 14 a watan Augusta, daga 1200.

Ko da yake a kan samu karuwar masu dauke da zazzabin cizon sauron yawanci a lokacin damuna, yadda adadinsu ya karu a yanzu ya sabawa kowanne lokaci.

Zazzabin cizon sauron dai shi ne musabbabin mutuwar yara da dama a kasar ta Chadi.