Babban jami'i a China zai sha dauri

Image caption Yang Dacai gaban kuliya

An yanke wa wani jami'in gwamnatin China, hukuncin daurin shekaru 14 a kurkuku, bisa laifin cin hanci.

Kafofin yada labaran gwamnatin China, sun ce an sami Yang Dacai ne da laifin karbar cin hanci, tare da mallakar kadarori masu yawa, amma ba'a san asalinsu.

Shi dai Mr Yang ya janyo fushin jama'a a China a kwanakin baya, yayinda aka ga hotunansa yana murmushi a wani wuri da aka yi wani hadarin mota inda jama'a da dama suka rasa rayikansu.

A hotunan ne ma aka gano cewa yana sanye da wani agogon hannu mai tsadar gaske.

Wannan al'ammari dai ya nuna yadda masu amfani da Intanat a China suke taka rawa wajen fallasa jami'an gwamnati da ke da hannu a cin hanci da rashawa.