Rikicin Syria zai kankane taron G20

Image caption Rasha dai ba ta goyon bayan yunkurin Obama na kai ma Syria hari.

Shugabanin kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya na taruwa a birnin St. Petersburg na kasar Rasha domin taron kolinsu na shekara-shekara wanda ake farawa ranar Alhamis.

Ana ganin batun rikicin Syria da kuma sabanin ra'ayin tsakanin Rasha da Amurka ne za su mamaye ajandar taron na kwanakki biyu.

Shugaban Amurka Barack Obama na cewar gwamnati a Damascus ta karya dokar kasashen duniya ta hana amfani da makamai masu guba kuma kai mata hari, kare dokar ta kasa da kasa ne.

Yayin da shi kuwa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce harin da Amurka za ta kai ma Syria ba tare da amincewar majalisar dinkin duniya ba ne zai zamo karya dokokin kasa da kasa.

Baraka mai fadada

Ra'ayoyin shubannin biyu sun yi hannun riga da juna kenan, kuma ga alamu wannan barakar da ke kara faddada ce za ta mamaye tattaunawar da za a yi a taron kolin kungiyar G20 na bana.

Duka shugabannin biyu na da abokan kawancen da za su goyi bayansu a wajen.

''Sai dai in da damben yake dai shi ne masu ra'ayin na tsaka-tsaka, wato wadanda ke nuna damuwa kan an yi amfani da makamai masu guba, kuma a hannun guda suke fargabar abin da zai biyo baya idan aka dauki matakin soji.'' inji wata wakiliyar BBC a birnin.

Babu dai bangaren da ga alamu zai samu rinjaye cikin sauki, kuma babu yiwuwar samun sasantawar da za ta kai ga rage barakar.

Karin bayani