Majalisar Dattawa ta goyi bayan Obama

Image caption Ya zuwa yanzu dai 'yan majalisa 23 ne kawai suka ce zasu goyi bayan kudurin.

Wani kwamitin majalisar dattawan Amurka ya amince da amfani karfin soja kan Syria, domin mai da martani ga kai hari da makamai masu guba da take zargin gwamnatin Assad da yi.

Kwamitin mai kula da hulda da kasashen waje, ya amince da daukar matakin ne ta hanyar jefa kuri'a, inda wakilai 10 suka goyi baya bakwai suka nuna adawa.

Yanzu dai kwamitin ya tura kudurin zuwa ga babban zaure majalisar domin jefa kuri'a watakila a makon gobe.

Sai dai duk da goyon bayan da ya samu a kuri'ar da kwamitin ya yi ranar laraba, babu tabbas kan makomar kudurin a babban zauren majalisar, kuma dole ita ma majalisar wakillan kasar ta amince da shi kafin ya zama doka.

Karin bayani