G20: Amurka ta soki Rasha kan Syria

Image caption Farayin Ministan Italiya Enrico Letta ne ya tabbatarda samun rarrabuwar kawunan a shafinsa na Twitter.

Kawunan shugabannin kasashen kungiyar G20 sun rabu kan batun Syria a karshen rana ta farko ta taron kolin da suke yi a Rasha.

Wata majiya ta ce zaman dar-dar tsakanin Shugaba Barack Obama na Amurka da Vladimir Putin na Rasha ya hauhawa ta yadda har sai da aka sauya yadda aka jera kujeru zama a zauren taron domin a sa tazara tsakaninsu.

Farayin Ministan Burtaniya David Cameron ya ce kasar sa ta samu sabuwar shaidar da ke nuna cewar gwamnatin Syria ta yi amfani da gubar sarin kan fararen hulla.

Yayinda Shugaban na Rasha Vldamir Putin ya sake nuna shakku ga ikrarin da kasashen yamma ke yi cewar suna da shaidar da za ta iya zama hujjar daukar matakin soja, inda ya zargi sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da zabga karya yayinda yake kokarin neman goyon bayan majalisar dokokin kasar sa.

'' Daukar matakin soji na gaban kai ya sabawa dokokin kasa-da-kasa da tarbiyyar dangatakar kasashe, kuma haka zai kara dagula lamarin na Syria kuma ya kara kawo hargitsi a yankin Gabas ta Tsakiya.'' Inji Hong Lee Ministan harkokin wajen kasar Sin.

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle, ya ce kamata ya yi a baiwa Kotun Hukunta Manyan Laifukka ta duniya aikin duba zargin na amfani da makaman guba a Syria.

Karin bayani