Ambaliya: Gwamnatin Nijar ne neman taimako

Image caption Ambaliyar ruwa a Nijar

Gwamnatin Nijar ta kaddamar da wani kiran neman agaji daga kasashen duniya, domin bullo wa matsalar ambaliyar ruwan da aka yi fama da ita a sassa daban-daban na kasar a 'yan kwanakin nan.

Wata sanarwa da fadar Pirayi ministan kasar ta bayar, ta ce gwamnatin kasar ba ta da karfin da za ta biya bukatun dukannin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa da kuma rage illolin da matsalar ta haddasa a kan muhalli.

Sanarwar ta ce ambaliyar ta haddasa hasarar rayukan mutane 26, kuma ta shafi mutane fiye da dubu 75 , tare da lalata eka dubu 32 na gonaki.

Karin bayani