Najeriya da Kenya sun kulla yarjejeniya

Image caption Shugaba Kenyatta da Shugaba Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da takwaransa na Kenya Shugaba Uhuru Kenyatta sun rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi.

Sa hannun dai ya biyo bayan wata ganawa ce da shugabannin biyu suka yi a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, da nufin karfafa alaka a tsakanin kashensu.

An kuma sa ran idan an jima da yamma shugaban na Najeriya zai yi jawabi a gaban majalisar dokokin kasar Kenya.

Shugaba Jonathan na ziyarar kwanaki uku ne a Kenya tare da wata tawagar 'yan kasuwa don duba hanyoyin hambaka kasuwanci tsakaninsu.

Karin bayani